Wed. Apr 2nd, 2025

Ƙungiyar Lauyoyi Reshen Ungogo Sun Yi Allah-Wadai Da Kisan Matafiya A Edo

By Saleh Aliyu Mar 31, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya jihar Kano reshen Ungogo ta nuna mutuƙar damuwarta da yin Allah-wadai bisa kisan gilla da aka yi wa matafiya da suke wucewa ta garin Edo.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar lauyoyi na Kano reshen Ungogo, Barusta Ahmadi Abubakar da aka raba wa manema labarai.

Ya ce wannan kusan gilla yana nuna take haƙƙin ɗan’adam na ‘yancin rayuwa cikin walwala kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar Nijeriya ya tabbatar.

Ya yi nuni da cewa waɗannan rayuka da aka kashe na waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba, hakan ya ci karo da kare haƙƙin ɗan’adam da tsarin rayuwa ta gari.

Ƙungiyar lauyoyin ta ƙasa Kano reshen Ungogo ta yi kira ga gwamnati a kan ta biya diyya ga iyalan waɗanda aka kashe ta, kuma tabbatar waɗanda suka aikata laifin an kama su an gabatar da su a gaban shari’a domin su girbi abin da suka aikata.

Sannan sun yi kira ga gwamnati ta samar da tsaro ga matafiya da ‘yan ƙasa ta kuma yi ƙoƙarin gano dalilai da suke jawo faruwar irin waɗannan abubuwa marasa daɗi domin a yi maganinsu.

Barista Ahmad Abubakar Gwadabe ya ce a matsayinsu na lauyoyi za su cigaba da tabbatar da ganin an kare dukkan wani haƙƙin ɗan’adam da ƙoƙarin kare haƙƙin ‘yan ƙasa ba tare da nuna bambancin ƙabila ko ɓangaranci ko bambancin addini ba.

Ƙungiyar lauyoyi ta miƙa ta’aziiyya ga iyalan mamatan da iftila’in ya rutsa da su da roƙon su zama masu haƙuri da juriya da bin doka a koyaushe.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *