Tue. Apr 1st, 2025

Ƙungiyar Hausawa Masu Sayar Da Kayan Gini A Kano Sun Zaɓi Sabbin Shugabanni

By Saleh Aliyu Feb 16, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Ƙungiyar Hausawa masu sayar da kayan gini na kan titin Faransa a yankin Sabon Gari a ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano sun gudanar da zaɓen sabbin shugabannin karo na farko.

An yi zaɓen ne ƙarƙashin shugabancin Alhaji Ibrahim Abdullahi Sani, wanda ya ce an yi zaɓe cikin nasara ‘yan takara sun yi abin da ya dace da waɗanda suka yi nasara da waɗanda ba suyi ba an haɗu an tafi cikin fahimtar juna dama a wuri ɗaya ake zaune, sannan akwai wayewa a tsakani ba saɓani.

Ibrahim Abdullahi ya ce, dama kafin zaɓen sun tattara masu ruwa da tsaki na zaɓen sun wayar musu da kai a kan cewa zaɓe ba ƙarfi ko dabara ba ne, Allah ne mai ba da mulki, kuma tunda aka fara zaɓe ba wani abu da aka samu game da ƙorafi ko wani abu na ba daidai ba, sannan duk an bi ƙa’dojin zaɓe.

Zaɓen an gudanar da shi ne a gurabe 12 na ‘yan takara bisa sanya idanun jami’an ma’aikatar kasuwanci ta jihar Kano ƙarƙashin mataimakin Darakta Ibrahim Abubakar Kabara, wanda ya tabbatar wa zaɓaɓɓun nasara bayan kammala zaɓen da aka gudanar bisa sa idon jami’an tsaro daban-daban da ‘yan jarida.

Isah Umar ne ya sami nasarar zama zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar da ƙuri’u 192.

Daga cikin waɗanda suka yi nasara akwai Kamalu Aliyu Jami’in hulɗa da jama’a da ƙuri’u 199. Mataimakin jami’in walwala Abdullahi Sulaiman da ƙuri’u 236. Sakataren kuɗi Kamilu Abubakar da ƙuri’u 172. Mataimakin sakataren ƙungiya Khalpha Awwal da ƙuri’u 326. Sakatare Kamal Sharif da ƙuri’u 169. Jami’in walwala Aliyu Manta da kuri’u 181 da a sauran waɗanda suka yi nasara.

Sabon shugaban ƙungiyar Isah Umar a jawabinsa bayan tabbatar masa da samun nasara, ya gode wa Allah da al’umma da suka zabe su da rokon Allah ya basu kwarin gwiwa domin tabbatar abin da suka alƙarwanta ‘yan ƙungiyar lokacin neman zaɓe.

Ya yi nuni da cewa, “Akwai abubuwa na ƙalubale da masu sana’ar kayan gini suke fuskanta shi ne ya sa ma muka shiga zaɓen. Mafi muhimmanci shi ne yadda kasuwancinmu ke yin baya. Akwai abubuwa da ya kamata mu haɗu don ciyar da kasuwar gaba, amma saboda babu tsayayyen shugabanci ba mu sami wannan damar ba, amma yanzu mun ɗaura ɗamara a kan waɗannan abubuwa da yardar Allah, kuma za mu yi nasara.”

Sabon shugaban Isah Umar ya jaddada cewa, “In Allah ya so ƙungiyar za ta zauna da ƙafarta da samar mata da ofis don gudanar da ayyuka. Duk shekara za mu fito mu yi wa mutane bayani a kan irin nasarori da muka cimma da yardar Allah.”

Ya ja hankalin waɗanda suka shiga zaɓe ba su kai ga yin nasara ba su zo a haɗu domin cigaban harkokinsu na kasuwanci.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *